Monday, April 13
Shadow

Rikicin jam’iyyar ADC ya munana a jihar Adamawa tsakanin Binani da Babachir

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa, rikicin jam’iyyar ADC ya munana tsakanin Aishatu Dahiru Binani da Babachir David Lawal.

Rikicin yayi kamari ta yanda yanzu haka Binani da Elisha Abbo zasu yi zama da magoya bayansu dan yanke shawarar ci gaba da zama ko ficewa daga jam’iyyar ADC.

Hakan na zuwane yayin da magoya bayan Binani ke ta kira a gareta da cewa, ta fice daga jam’iyyar ta ADC.

Magoya bayan Binani na cewa, shekaru 10 tana rike da jam’iyyar amma gashi daga baya su Babachir sun zo zasu kawo tarnaki.

Yanzu dai abin jira shine a ga matakin da Binani zata dauka

Karanta Wannan  Hotuna: Kwalliyar Sallah ta Tauraruwar me taimako kuma 'yar Kasuwa, Laila Usman da Mijinta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *