Ruwan kwakwa da zuma na da matukar amfani ga budurwa ko ma a ce ga mata gaba daya.
Da farko dai hadin ruwan kwakwa da zuma na maganin infection na mata,saboda yana da antiseptic wanda ke kashe abubuwan dake kawo infection da kaikai a gaban mace.
Hakanan wannan hadi na ruwan kwakwa da zuma yana da matukar amfani wajan gyaran gashi, musamman wanda ya fara zubewa ko kuma yake karyewa,idan aka yi amfani da wannan hadi za’a ga abin mamaki.
Wannan hadi kuma yana da matukar amfani wajan kara karfin kuzari. A yayin da ake jin kasala ko kuma ana son yin ani aiki ko an yi aikin an gaji, ana iya shan ruwan kwakwar da zuma dan samun kuzari.
Hakanan wannan hadi yana taimakawa wajan hana tsufan fata.
Hakanan yana taimakawa daidaituwar jiki, ba za’a yi kiba sosai ba kuma ba za’a rame sosai ba.