
Omoyele Sowore, dan Fafutuka kuma mamallakin Jaridar Sahara Reporters ya bayyana cewa, a baya yasha gargadin dan Damben Najeriya, Anthony Joshua kan ya daina shigewa ‘yan siyasar Najeriya amma yaki.
Yace gashinan yanzu ta fito fili, yayi hadari babu wani taimakon gaggawa na musamman da ya samu.
Sowore yace shuwagabannin Najeriya cin hanci da rashawa ya musu yawa sannan kuma azzalumaine.
A karshe yace yana taya AJ fatan Allah bashi Lafiya.