
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, sai Arewa ta hada kai da ‘yan kudu dan ceto Najeriya daga halin data tsinci kanta.
El-Rufai ya bayyana hakane a yayin ziyarar gaisuwar da ya kai Jihar Delta ta gaisuwar mutuwar Edwin Clark.
El-Rufai wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yawa jagora zuwa jihar Delta yace Arewa ta sha hada kai da kudu dan cimma burikanta na siyasa.