
Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa, duka ‘yan Izala suna kan irin maganar da Malam Lawal Triumph ya fada.
Ya jawo hankalin Gwamnatin Kano da cewa, Kada ta siyasantar da harkar Addini.
Yace idan kuwa an ce za’a rika kama masu irin wannan ra’ayi to saidai idan kowa da kowa mutanen Ahlussunah za’a kama.