Shahararren ɗan jaridar nan, Jaafar Jaafar ya zargi mataimakin shugaban majalissar dattijai Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano.
Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Jaafar Jaafar na zarge-zargen ne ta cikin shirin “Fashin Baƙi” da suka saba gabatarwa mako-mako.
A cewar Jaafar “Mutane da yawa suna tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Suna shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi. Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗansanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu. Muna da bayanan sirri”. Jaafar Jaafarya ce.
Me zaku ce?