
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti ta kasa kawo hujjojin kan zargin da take masa na cewa, ya nemeta da lalata.
Ya bayyana hakane ta bakin lauyansa, Dr Olisa Agbakoba (SAN) yace dalili ma kenan na yin magamganin da ta yi kwanannan.
Yace wani karin abin mamaki shine, Sanata Natasha Akpoti ta goge rubutun da ta yi na zargin da take masa a shafinta na sada zumunta.
Yace wani karin abin dubawa shine Sanata Natasha Akpoti tace a shekarar 2023 ne Ya nemeta da lalata, amma bayan nan, ta bishi sun je taruka da yawa a ciki da wajen Najeriya a shekarar 2024.
Yace a wajan wasu tarukan ma har hotunan Selfie take daukarsu tare kuma ta dora a kafafen sadarwa.
Dan haka ya nemi Sanata Natasha Akpoti ta janye zargin da take masa.