Saturday, May 24
Shadow

Sanatocin Jihar Kebbi 3 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Hukumance a zaman majalisa na yau

Mai girma Sanata Dakta Muhammad Adamu Aliero, CON, mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, tare da Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi na Kebbi ta Arewa da Sanata Musa Garba Maidoki na Kebbi ta Kudu, sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Sanatocin sun bayyana wasu dalilai da suka sa suka bar PDP kamar haka:

  1. Rashin Jagoranci: Sun nuna damuwa game da rashin ingantaccen jagoranci a cikin jam’iyyar PDP.
  2. Rigimar Cikin Gida: Sun ce rikice-rikicen cikin gida da ke ci gaba da faruwa a jam’iyyar ya taka rawa matuka a yanke shawarar da suka dauka.
  3. Goyon Bayan Jagorancin APC: Sanatocin sun bayyana goyon bayansu ga jagorancin Mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu, inda suka ce sauya shekar da suka yi zuwa APC zai taimaka wajen dorewar kyakkyawan mulki da ci gaban Najeriya gaba ɗaya. Senator Aliero Media & publicity
    13/05/2025.
Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata mata ta fito tace ita Annabiya ce kuma Akwai Karama akanta, Duk wanda ya shafa zai yi kudi, mutane na ta tururuwar zuwa shafa Kanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *