Sanatocin jihar Kebbi uku sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya da Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta Arewaa, da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta Kudu, suna shirin komawa jam’iyyar, a cewar shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan ya biyo bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.