Tauraron Fina-finan Hausa, Sani Musa Danja ya bayyana cewa bai kamata ana amfani da siyasa wajan kawo rabuwar kai a jihar Kano ba.
Sani Musa Danja ya bayyana hakane a wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Yace duka sarakunan nan ‘yan uwan junane kuma duka mutanen kirki ne, bai kamata a zo a kawo wani abu da zai iya kawo gaba ko rashin jituwa a tsakaninsu ba.
Ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano data gabata ce, watau ta Umar Abdullahi Ganduje ce ta kawo wannan matsala.
Ya bada shawarar yin abinda ya kamata dan kawo zaman lafiya me dorewa a jihar ta Kano