Saturday, July 13
Shadow

Ya kamata majalisar tarayya ta yi dokar da zata hana ‘yan siyasa saukewa da wulakanta Sarakai>>Sheikh Dahiru Bauchi

Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa kan sauke Aminu Ado Bayero da Gwamnatin jihar Kano ta yi.

A jawabin da ya fitar ta bakin kakakinsa, malamin yace yana baiwa majalisar tarayya shawara ta yi dokar da zata hana ‘yan siyasa saukewa da wulakanta sarakai.

Gwamnatin jihar Kano, Karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero inda ta mayar da Sarki Muhammad Sanusi II akan kujerar.

Lamarin ya jawo tashin hankula a jihar ta Kano inda Sarki Aminu Ado Bayero ya dawo yake ikirarin cewa shima sarkine.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Ana zargin kwaikwayar sa hannun Babban alkalin kotun Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya wanda yace a sauke Sarki Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, Kalli Hotunan dake tabbatar da hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *