Thursday, November 12
Shadow

Sarkin Katsina na ta shan jinjina saboda yanda ya tsagewa Kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubu da suka kai masa ziyara Gaskiya

Me martaba sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman na ta shan Yabo saboda yanda ya tsagewa Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da suka kai masa ziyara Gaskiya.

A cikin wani Bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta an ji Sarki na ce musu kada su yi karyar abinda suka san ba zasu iya yi ba.

Sannan ya koka musu kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma inda yace an hana mutane Noma.

Hakanan yace An kulle kamfanoni da yawa a Arewa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Iyayen wannan yarinyar na ta shan yabo saboda ta ki amincewa dan ajinsu ya mata rubutu a jikin kayanta irin wanda ake yi bayan an kammala makaranta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *