
Tun ranar 28 ga watan Disamba na shekarar 2025 ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Najeriya zuwa Turai.
Shugaban ya kuma halarci taron kasashen Duniya dake gudana a kasar UAE.
Yanzu sati 3 kenan shugaba Tinubu baya Najeriya.
‘Yan Najeriya da yawa a kafafen sada zumunta sun fara tambayar shin ina shugaban kasar ya shigane?
Wasu na tambayar Allah sa dai Lafiya.
Rahotanni sun bayyyana cewa, Kwanakin shugaba Tinubu 961 akan Mulki saidai a cikin wadannan kwanakin ya shafe wanaki 240 a kasashen waje.
Watau a duk cikin kwanaki 4 da yayi yana mulki, kwana daya yayi shi ne a kasashen waje.