Akwai zafi da daci da bakin ciki da dana sani idan saurayi ya yaudari budurwarsa.
Da farko zaki rika jin me zaki yi dan ki rikeshi kada ya barki, watakila ki rokeshi, watakila ki rika addu’a, zaki iya yin kuka a gabanshi ko ke kadai a daki.
Wannan yanayi akwai radadi da zafi.
Saidai idan zaki iya, kada ki yawaita magana da kowa idan kika shiga wannan yanayi, dan kuwa a wannan yanayi duk wanda kike magana dashi zaki iya gaya masa sirrikanki wanda bai kamata wani ya sani ba. Sai daga baya ki rika dana sani.
A irin wannan yanayi zaki ji jikinki yayi sanyi, zaki ji kamar baki da amfani, zaki ji kin rude, zama ki iya jin dama ki mutu.
Tambaya ta farko shine, Saurayinki da ya rabu dake ya taba yin zina dake?
Tambaya ta biyu ya miki ciki?
Tambaya ta uku, yana da hotunanki na batsa?
Idan duka baya dasu, bai taba miki ciki ba, bai da hotunanki na batsa, bai taba yin zina dake ba, to kinsha.
Abinda zan baki shawara anan idan kin yi magana dashi kin tabbatar ya rabu dake bai son ci gaba da yin soyayya dake, to ki kyaleshi.
Nasan abune me wahala amma ki daure, ki goge lambar wayarshi daga wayarki, ki raba kanki da duk wani abu da zai iya tuna miki dashi.
Ki yawaita Zikiri, ki mayar da lamarinki ga Allah.
Watakila zaki iya yin tunanin zaki samu wani saurayin kamarshi kuwa? Insha Allahu zaki samu:
Ki tuna irin soyayyar da iyayenki ke miki tun baki san kanki ba, baki da wayau suka reneki, suka baki abinci, suka miki sutura, bayan hakane fa kika hadu da wannan saurayi, to lallai ya kamata ki yi dauriyar rabuwa dashi idan har da gaske yake ya daina sonki.
Ki tuna irin zumunci da soyayya dake tsakaninki da ‘yan uwanki, ki tuna wasa da kuka rika yi ko kuke yi yayin da kuke tasowa.
Ki tuna abokai na gaskiya da irin yanda suke daukarki da muhimmanci.
Ki tuna nasarorin da kika samu a rayuwa.
Ki tuna abubuwa masu muhimmanci da kike son cimma a rayuwarki, dan haka rabuwa da saurayi bai kamata ta sa kiji baki da muhimmanci ba.
Kina da muhimmanci da mutunci da kima a idanun mutane da yawa, ki baiwa kanki kwarin gwiwa da karfin zuciya.
Kada ki rika zama a daki kina tunani, ko da baki da gurin zuwa, ki tashi ki yi aikin gida ko wasu abubuwan da zasu amfaneki ko su amfani wani dake tare dake.
Hakan zai sa ki ji saukin Zafin rabuwa da saurayinki da kike ji.
Idan kuma Ya taba yin zina dake, to lallai kin tafka babban kuskure, sa’arki daya shine idan ciki bai shiga ba.
Idan kin tabbata ya rabu dake baya son ci gaba da soyayya dake, kamar yanda nace a sama, kada ki ci gaba da kiranshi kuma kada ki baiwa kowa labarin zinar da yayi dake, saboda bayar da labarin zai zama abin muzantawa a gareki nan gaba kuma kamar kina alfaharine da abinda ya faru, Allah ya rufa miki asiri kun yi ta tsakaninku babu wanda ya sani, dan haka kada ki gayawa kowa, koda kawarki ce wadda kika yadda da ita.
Ki nemi yafiyar Allah, dan kuwa kin aikata Alfasha, ki tashi cikin dare ki yi kuka ki nemi Allah ya yafe miki da niyyar ba zaki sake aikatawa ba, kuma ki bi shawarar da na bayar a sama, dan dawowa kanki da kwarin gwiwa da sanin muhimmancin kanki.
Idan kuwa ya rabu dakene kuma ya miki ciki: To lallai kina cikin lamari me tsanani, ba zan baki shawarar zubar da ciki ba, kuma ba zan ce ki haifeshi ba.
Anan ki sameshi ku yi shawara akan mafitarku, tunda dai ciki nashine, mutane biyu ne zasu iya baku shawara akan abinda ya kamata ku yi, ku sami babban malami me mutunci wanda ba zai tona muku asiri ba ya baku fatawa, hakanan ku samu likita wanda ya san abinda yake shima ya baku shawara, kada ku gayawa kowa, bayan wadannan.
Abu na gaba shine idan yana da hotuna ko bidiyonki na batsa shima kin tafka kuskure babba, dan kuwa Allah ne kadai zai iya taimakonki a wannan lamari.
Idan saurayin naki da ya rabu dake dan mutunci ne kuma yana da hankali zai iya gogesu ba zai yada ba. Kema kina iya kiranshi ki rokeshi ya goge kada ya yadasu ko ya gayawa wani.
Idan kuma kina da wata hanya da zaki iya bi ki goge hotunan ko bidiyon daga wayarsa shima zaki iya bi amma duk da haka babu tabbacin basu yadu ba dan watakila ya riga ya nunawa wasu abokansa.
Hakanan ki roki Allah yafiya, kuma kibi shawarwarin da na bayar a sama dan dawowa kanki da kima da sanin darajar kai.
Allah ya kyauta, ya hada kowa da masoyi na gaskiya.
Muna godiya