
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sabuwar jam’iyyar da ya koma, SDP, ta fi buƙatar ta tara mambobi daga tushe ba wai manyan ƴan siyasa ba.
El-Rufai, wanda ya fice da ga jam’iyyar APC a watannin baya, ya baiyana hakan ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a jihar Kano a yau Litinin.
A cewar sa, SDP jam’iyya ce da ke rajin farfaɗo da dimokuraɗiyya tun daga tushe domin gyaran Nijeriya.
“Mu ba mu damu da tara manyan ƴan siyasa a SDP ba. Mun fi son mu ga kamar mutane miliyan 3 sun yi rijista a SDP.
“SDP jam’iyya ce da za ta baiwa kowa dama iri ɗaya. Ba za mu bari wani mutum ɗaya ya riƙa iko da jam’iyyar ba.
“So mu ke yi mu gyara dimokuraɗiyyar kasar nan,” in ji El-Rufai, yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai.
Hakazalika El-Rufai ya ce SDP na da wani sashe da ke yin nazari akan cigaban Najeriya da gyaran tattalin arzikin ƙasa da samar da tsaro idan Allah Ya sa ta samu nasara a zaɓen 2027.
Ya kara da cewa yanzu ba maganar ƴan takara ake yi ba a SDP, sai dai batun tara ƴan jam’iyya da za su karfafa ta.