
Turaruwar fina-finan Kudu, Destiny Etiko da aka saba gani sanye da kaya tsirara-tsirara a cikin watan Azumi sai gata sanye da Hijabi.
Abin ya baiwa masoyanta mamaki inda akai ta tambayarta menene dalili.
A cikin wani bidiyo data wallafa a shafinta na sada zumunta, ta fadi daliinta na yin hakan.
Tace wani fim ne ta fito a ciki a matsayin bahaushiya, shiyasa ake ta ganinta sanye da Hijabi kwana biyu.