Daga Comr Nura Siniya
Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya daga jihar Katsina Sheikh. Mal. Ismail Zakariya Alkashnawy, ya kammala karatun sa na digirin digirgir (PhD) a ɓangaren Larabci a jami’ar Annahdha International University da ke Niamey a ƙasar Niger.
Haziƙin Malamin Dr. Alkashnawy, ya nuna hazaƙa sosai, yayin da ya kammala karatun da mataki mafi daraja (First Class).