Wednesday, January 15
Shadow

Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci.

Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar – ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu – suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata.

Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje.

A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau.

Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi tsayawa su yi aiki a ƙasar.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar canza taken Najeriya

“Likitocin Najeriya na cikin zuciyar shugaba Bola Ahmed Tinubu. Akwai abubuwa da dama da ya yi musu tanadi, musamman ga waɗanda suka zaɓi tsayawa su yi aiki a ƙasarsu,” in ji Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *