Tuesday, May 6
Shadow

Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya, Abdullahi Sule ya ce wasu na son yin amfani da rashin “zuwan tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari Abuja” domin nuna cewa akwai ɓaraka tsakaninsa da shugaban ƙasar mai ci, Bola Tinubu.

Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin da alamu suka bayyana cewa an samu ɓaraka tsakanin makusantan tsohon shugaban ƙasar, waɗanda suka kasance a jam’iyyar CPC, wadda Buhari ya jagoranta kafin shiga haɗakar da ta samar da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

A baya-bayan nan wani ɓari na ƴaƴan tsohuwar jam’iyyar ta CPC sun bayyana mubaya’arsu ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, sai dai kwanaki kaɗan bayan hakan wasu ƴaƴan tsohuwar jam’iyyar kuma waɗanda ke da matuƙar kusanci da Buhari sun nesanta kansu daga mubaya’ar.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis

Haka nan sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda shi ma makusancin tsohon shugaban ƙasar ne ya ƙara ɗora ayar tambaya kan alaƙar da ke tsakanin tsohon shugaba Muhammadu Buhari da kuma shugaba mai ci Bola Tinubu.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Abdullahi Sule ya ce “maganar cewa abubuwa sun yi tsamari duk kuskure ne…don ba ya zuwa Abuja shi ne za a ce ba ya tare da wannan gwamnatin, ina jin wannan kuskure ne.”

Haka nan gwamnan ya musanta batun cewa sun ziyarci tsohon shugaban ƙasar da nufin shawo kansa kada ya fice daga jam’iyyar.

An riƙa zargin cewa wasu daga cikin gwamnonin sun kai ziyara wa tsohon shugaban ƙasar a ƙoƙarin tabbatar da goyon bayansa ga Tinubu, sai dai Sule ya: “mu dai ba mu yi maganar dannan ƙirji a wurin ba…ba a yi haka ba.”

Karanta Wannan  Yan bìndigà sun sace dalibai 4 maza na Jami'ar FUDMA a jihar Katsina

Al’amura na ƙara zafi a siyasar Najeriya bayan kokawar da al’ummar ƙasar ke yi kan wahalhalu sanadiyyar matsin tattalin arziƙi bayan wasu manufofi na gwamnatin Shugaba Tinubu.

Wannan ya bai wa ƴan adawar siyasa damar sukar gwamnatin, inda ake ganin alamun suna ƙoƙarin yin haɗaka domin ƙalubalantarsa a babban zaɓen ƙasar na gaba da za a gudanar a shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *