Thursday, January 9
Shadow

Shugaba Tinubu ya canja ra’ayi kan maganar sauya Fasalin Haraji

Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya la’akari da wasu sharuda daga gwamnoni akan maganar canja fasalin harajin kasa.

Kudirin dokar canja karba da raba harajin wanda ke gaban majalisar tarayya ta fuskanci koma bayan da rashin karbuwa musamman ga gwamnonin Arewa inda hakan yasa dole majalisar ta dakatar da zartar dashi inda a yanzu ake bi dan jin ra”ayin jama’a.

Duk da sukar da wannan kudirin canja haraji ke fuskanta, shugaba Bola Ahmad Tinubu ya jajirce akan cewa babu gudu ba ja da baya kan lamarin.

Karanta Wannan  ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

Bwala a yayin hira da gidan talabijin na ChannelsTV ya bayyana cewa, maganar kudirin dokar canja fasalin haraji babu gudu ba ja da baya kuma majalisa zata amince da kudirin.

Yace abinda gwamnonin Arewa ke yi suna neman a zauna a Teburin tattaunawa ne inda Shugaban kasa zai amince da wasu sharuda suma su amince da wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *