
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kokarin karfafa tattalin arzikin Najeriya ya hana sayo kayan da ake iya yinsu a cikin gida daga kasashen waje.
Majalisar zartaswa tuni ta amince da wannan kudirin a zamanta na ranar Litinin inda aka bayyana cewa an yi hakanne dan karfafa masana’antun gida Najeriya.
Da yake magana ga manema labarai bayan zaman, ministan yada labarai, Mohammed Idris yace an dauki wannan mataki ne dan karfafa amfani da kayan da aka kerasu a cikin gida.
Yace sun kwaimwayi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ne a kokarin da yake na karfafa masana’antun kasarsa ta Amirka