
Fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yanke hutun da yake ba tare da kammalawa ba ya dan dawowa gida Najeriya.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Yace shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya ranar Talata dan ci gaba da ayyukan raya kasa.