Monday, December 16
Shadow

Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyara Kasar Sin Domin Haɓaka Tattalin Arziki Da Kayayyakin More Rayuwa

A farkon watan Satumba ne shugaba Bola Tinubu zai fara wata ziyara zuwa kasar Sin, da nufin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da samar da ababen more rayuwa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa game da ziyarar a ranar Talata.

A cewarsa, shugaban zai kai ziyara zuwa kamfanin Huawei Technologies, da kuma Kamfanin harhada jiragen kasa na CRCC domin kammala aikin titin Ibadan zuwa Abuja na babban layin dogo na Legas zuwa Kano.

Da yake jaddada mahimmancin tafiyar shugaba Tinubu ga ‘yan Nijeriya, Ngelale ya bayyana cewa, jerin ziyarar da shugaban zai yi a birnin Beijing zai haifar da fa’ida cikin gaggawa ga tattalin arzikin Nijeriya da al’ummar kasar baki daya.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Mansurah Isa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *