
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya baiwa ma’aikatar yaki ta kasarsa umarnin a dawo a ci gaba da gwajin makamin kare dangi, watau Nokiliya.
Shugaban yace idan dai wasu kasashe zasu rika yin gwajin bai ga dalilin da zai hana kasar Amurka itama ta rika yin irin wannan gwajin ba.
Saidai masu sharhi sun ce abinda suka fahimta shine shugaban ba yana nufin a rika harba makamin bane, yana nufin a rika gwadawa Duniya Kwajin kasar Amurka ne.
Hakan na zuwane a yayin da shugaba ke kan hanyar zuwa kasar China.
Saidaj wasu masana sun ce gwajin makami wanda Nokiliya ke karfafashi wanda kasar Rasha ta yi ne ya tunzura shugaba Trump.
Shekaru 33 kenan rabon da kasar Amurka ta yi gwajin makamin na Nokiliya.
Akwai dokokin kasa da kasa da suka hana yin gwajin.