Monday, April 21
Shadow

Shugaban riƙon ƙwarya a Rivers ya isa fadar Shugaba Tinubu

Shugaban riƙon ƙwarya na Rivers, Vice Admira Ibok-Ete Ibas da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa kan wannan mukamin ranar Talata ya isa fadar shugaban ƙasa.

Da alama zuwan nasa na da alaƙa da dokar ta-ɓacin da Tinubu ya ƙaƙaba a Rivers bayan da jihar ta faɗa rikicin siyasa.

Tuni dai wannan mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya janyo mabanbantan ra’ayoyi inda al’ummar ƙasar da ƴansiyasa da ma masana ɓangaren shar’a ke ta tsokaci a kai.

Karanta Wannan  Dalilan da ya sa mata ke rububin rigar mama ta gwanjo a Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *