Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode ya bayar da umarni ga ‘yansandan kasarnan da su daura bakin kyalle na tsawon kwanaki 7 dan nuna alhinin rasuwar shugaban sojoji Lt. Gen. Taoreed Lagbaja.
Kakakin ‘yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Yace wannan matakine da aka dauka dan girmama tsohon shugaban sojojin da kokarin da ya nuna wajan yaki da matsalar tsaro.