
Shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin yin bincike dan gano gaskiyar ikirarin wani tsohon dansanda da yace an biyashi Naira Miliyan 2 a matsayin kudin sallama.
Hutudole ya ruwaito muku cewa, Bidiyon dansansan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ya jawo cece-kuce.
Dansandan wanda yayi ritaya da mukamin Superintendent of Police yace ba zai karbi Naira Miliyan 2 ba saboda ta masa kadan bayan shafe shekaru 35 yana aiki a matsayin dansanda.
Dansandan wanda yayi ritaya a watan October 1, 2023 yace hukumar kula da fansho na ‘yansanda ta sanar dashi cewa kudin sallamarsa Naira Miliyan 2 ne sannan akwai Naira Miliyan daya ta bashin kudin fansho da yake bi.
Kakakin ‘yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, shugaban ‘yansandan ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin.