Monday, December 16
Shadow

Sirrin tsayuwar nono ga budurwa

Mafi yawanci budurwa tana tasowa ne da nonuwanta a tsaye. Amma wsu dalilai sukan sa nonuwan su kwanta.

Saidai budurwa ta sani cewa, idan tana da karancin shekaru, misali, daga 10 zuwa 15 nonuwanta basu gama girma ba, dan haka kada ta damu kanta da tsayuwar nonuwa ko karin girmansu.

Ta dakata tukuna har sai jikinta ya kammala girma, nonuwan sun kammala fitowa gaba daya.

Mafi yawan lokuta Nonuwan mace suna gama girma ne idan ta kai shekaru 18, saidai wasu matan nonuwansu na kara fitowa waje su kara girma har zuwa su kai shekaru 20 zuwa 25.

dan haka idan mace tana tsakanin shekaru 10 zuwa 20 ko 25 kada ta yi gaggawar nemanaganin kara girman nono, ta jira tukuna ta ga nonuwan nata su gama girma.

Karanta Wannan  Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Kuma a sani mafi yawanci mata suna gadon girman nono ne a wajen iyayensu, idan mahaifiyarki kananan nonuw take dasu, to ana kyautata zaton kema kananan nonuwa zaki yi, hakanan idan kuma manyan nonuwa take da, kema zaki iya yin manyan nonuwa.

Idan kina son nonuwanki su tsaya,ki rika saka rigar mama yayin da kike aikin karfi ko motsa jiki. Masana aun bayyana cewa, a yayin da mace take motsa jiki ko take aikin karfi, nonuwanta suna reto ko suna sama da kasa, hakan yakan sa su kwanta.

Maganin hakan shine idan ana aikin karfi ko ana motsa jiki, a saka rigar mama wadda ta yi daidai da nonuwan.

Karanta Wannan  Gyaran nono lokacin yaye

Hakanan masana sun bada shawarar cewa idan ana son nonuwa su tsaya kada su kwanta, to idan mace tana zaune bata aikin karfi ko motsa jiki, kada ta rika saka rigar mama.

Masana sun bayyana cewa shan madara da motsa jiki suna kara taimakawa nonon budurwa su tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *