Friday, October 4
Shadow

Gyaran nono su tsaya

Akwai hanyoyin gyaran nono da yawa, a wannan rubutu zamu yi maganane akan yanda zaki gyara nonuwanki su tsaya.

Saidai kamin mu fara bayani,bari mu gaya muku abubuwan da a likitance aka tabbatar suna sanya nonuwa su zube.

Shekaru: Idan mace shekarunta suka fara ja, nonuwanta zasu zube.

Rashin Kuzari: Idan na fama da rashin kuzari wanda yawanci ke samo asali daga rashin samun ingantaccen abinci me gina jiki shima yana sanya nonuwa su zube.

Rashin Sha’awa: Idan ya zamana mace bata da sha’awa ta jima’i ko sha’awarta ta yi kasa sosai, bata damu da jima’iba, hakan yana iya kaiwa ga zubewar nono.

Karanta Wannan  Girman nono da hulba

Abinda ke jawo hakan shine yawanci rashin cin abinci me gina jiki da kuma rashin samun nutsuwa da aikin karfi.

Gravity: Yanayi ne da babu yanda mace zata yi indai tana raye sai nonuwanta zun kwanta.

Kibar data wuce kima: Mace me kiba sosai zata iya fuskantar zubewar nonuwa.

Manyan Nonuwa: Idan mace na da manyan nonuwa, zasu iya fara zubewa da wuri.

Idan mace ta haihu da yawa: Duk macen data haihu da yawa, nonuwanta zasu zube.

Rama me yawa: Idan ya zamana mace na fama da matsananciyar rama, nonuwanta zasu iya zubewa.

Shan Taba: Shan taba yana sanya nonon mace ya zube.

Karanta Wannan  Gyaran nono lokacin yaye

Abubuwan da basu sa nono ya zube

Shayarwa bata sanya nonon mace ya zube.

Hakanan rashin saka rigar mama baya sanya nonon mace ya zbe.

Saka Rigar mama wadda bata da kyau shima baiwa nono ya zube.

Yanda zaki yi gyaran nono su tsaya

Idan ana son a yi gyaran nono su tsaya to a kiyaye kada a yi kiba sosai,kada kuma a rame da yawa, a tsaya tsaka-tsakiya.

Idan za’a yi aikin karfi, ko za’a motsa jiki, a rika saka rigar mama. Amma idan ana zaune haka kawai ba lallai a saka ba.

Kada a sha sigari ko duk wani abin hayaki irin su wiwi.

Ba za’a ce kada mace ta haihu ba,amma yawan haihuwa yana sanya nonuwa su zube.

Karanta Wannan  Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Babbar hanyar tsaida nonuwa su tsaya tsaf itace hanyar tiyata amma fa tana da hadari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *