Wednesday, January 15
Shadow

Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba – Ambasada Wali

Sojoji Ne Suka Ƙaƙaba Mana Obasanjo Ba A Barmu Munyi Zabin Mu Ba – Ambasada Wali

Ɗaya daga cikin jigo a siyasar Arewacin Najeriya kuma tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali ya ce gabanin zaben shekarar 1999, sojojin da za su miƙa mulki ga farar hula ne suka ƙaƙaba wa ‘yan siyasa Cif Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a waccan shekarar.

Ambasada Wali wanda yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998, ya ce “lokacin PDP da aka je kulla yarjejiniya a Jos a shekarar 1998, wanda kuma a lokacin soja ne ke mulki, ba a bar mu mun zaɓi abin da muke so ba.”

Karanta Wannan  Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yace Ya Bada Umarnin Gyaran Dukkanin Hanyoyin Jihar Kano

“Da sai a ƙyale mu mu zaɓi wanda muke so. Amma haka ba ta samu ba. Ba don shigowar soja ba, suka dan saka hannunsu, watakila da Obasanjo bai zama ɗan takara ba”.

“Kuskuren da muka yi lokacin da aka kafa PDP, babu wanda ya nemi ya tsaya zaɓe a arewa sai Atiku. Wannan kuskure ne,” in ji Wali.

Ya ƙara da cewa a yanzu babu siyasar aƙida, ‘yan siyasa kawai neman takara suke yi ido rufe, shi ya sa suke sauya sheƙa zuwa waɗansu jam’iyyun a kowanne lokaci.

Ya ce “lokacin siyasa ce ta aƙida. Ɗan PRP ba zai yarda ya tsaya takara a NPN ba amma yanzu babu aƙida”.

Karanta Wannan  Yajin Aikin NLC:Lamura sun tsaya jik a Abuja

A cewar Ambasada Aminu Wali, lokacin jamhuriya ta biyu jam’iyya ce ke da ƙarfi ba zaɓaɓɓen shugaba na gwamnati ba, “shugaban jam’iyya ya fi gwamna ƙarfin iko a siyasa”, kamar yadda BBC ta rawaito.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *