Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe ‘yan ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi da ke addabar jama’a a waɗansu jihohin arewa maso yammacin kasar.
Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.
Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasar na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan, a hirarsa da BBC.
Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana ‘yan Lakurawan yin tasiri a arewacin kasar.
Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, inda suka yi masa bayani kan matakan da suka shirya ɗauka kan wannan ƙungiya.
“Ni ma sun yi mani bayani kuma na gamsu da shirinsu. Idan Allah ya yarda za a samu nasara nan da ɗan lokaci ,” in ji ministan.