Sojojin Najaria sun bayyana gagarumar nasarar da suka samu a shekarar 2024 inda suka ce sun kashe ‘yan Bindiga guda 10,937 inda suka kama guda 12,538.
Kakakin sojin Major General Edward Buba ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda yake bayani kan ayyukan da sojojin suka gudanar a shekarar 2024.
Hakanan yace sojojin sun kubutar da jimullar mutane 7,063 da aka yi garkuwa dasu.
Sannan aun kwace jimullar makamai 8,815 da Albarusai 228,004.