
Rundunar sojin Najeriya ta Operation Safe Heaven ta ce ta daƙile wani yunkurin kai hari a ƙauyen Teegbe da ke karamar hukumar Bassa na jihar Filato, tare da kashe ɗaya daga cikin maharan.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Nantip Zhakom ya fitar ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba 23 ga watan Afrilu, inda artabun da sojojin suka yi da maharan ne ya janyo wasu suka tsere.
“Wani mazaunin yankin ne ya kira mu ya faɗa mana abin da ke faruwa, daga nan dakarun mu suka garzaya wurin. Sun fafata da ƴan bindigar har ta kai ga kashe ɗaya daga cikinsu, tare da kama wasu mutum biyu waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu,” in ji Manjo Samson.
Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma samu nasarar kama wasu ƴan fashi uku a wani samame da suka kai hanyar Katnan- Buratali da ke yankin Wase.
Ya ce an samu mutanen da ake zargin ɗauke da wata bindiga da ake ƙera wa a cikin gida, kuma sun amsa cewa sun yin fashi tare da wasu ƴan uwansu a hanyar.