Monday, December 16
Shadow

Sowore ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar su je su kammala ginin rukunin gidaje 753 da gwamnati ta kwace a Abuja su ci gaba da zama a ciki saboda gidajen nasu ne.

Ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter.

https://twitter.com/YeleSowore/status/1863671862175166904?t=WysOD6GSPJtaBSMTjA6nFg&s=19

Gidajen dai a cewar hukumar EFCC sune kadara mafi girma da suka taba kwacewa tun bayan kafa hukumar.

Bayanan kotu sun nuna cewa, an kwace gidajenne daga hannun tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele saidai EFCC taking ambatar sunan tsohon gwamnan CBN din inda tace an kwace kadarorinne daga hannun wani tsohon jami’in gwamnati.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu ya sauka a China domin ganawa da Shugaban China Xi Jinping

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *