Friday, December 26
Shadow

Su Atiku, Peter, Obi da Amaechi na jam’iyyar ADC sun sakawa takardar Alkawari hannu cewa duk wanda yayi nasarar lashe zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar zasu mara mai baya

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Rahotanni daga jam’iyyar ADC na cewa, manyan ‘yan Adawa da suka hadu a jam’iyyar sun sakawa takardar Alkawari hannu cewa kowanene a cikinsu yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar zasu mara masa baya.

Daya daga cikinsu, Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Leadership.

Ya bayyana cewa amma sai idan an yi gaskiya wajan gudanar da zaben fidda gwanin ba’a yi magudi ba.

Saidai me magana da yawun jam’iyyar ADC din, Malam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa, bai san da maganar alkawarin ba amma zasu tabbatar an wa kowa Adalci.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Bayan da aka yi Allah wadai da lamarin, Ma'aikatar noma ta Najeriya ta dakatar da Shirin yin Azumi dan neman sa'ar wadatar abinci a Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *