Saturday, January 10
Shadow

Tanko Yakasai yayi kiran Arewa ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu saboda kokarinsa na tada komadar tattalin arziki na samar da sakamako me kyau

Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya yabawa Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda kokarin tayar da komadar tattalin arzikin da take.

A bayanin da ya yiwa ‘yan Jarida ranar Lahadi a Kano, Tanko Yakasai ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun fara samun sauki daga matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.

Yace farashin kayan masarufi da na man fetur na ci gaba da sauka.

Yakasai yayi kira ga ‘Yan Arewa dama Najeriya baki daya dasu ci gaba da baiwa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu goyon baya.

Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu na kokarin samar da ci gaban kasa kuma Arewa ba’a barta a baya ba a wannan kokari.

Karanta Wannan  Insha Allahu Daga Yau Ma Bar Darika Kuma Ina Mai Neman Afuwar Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi Da Iyalansa Da Dalibansa, Kuma Daga Yau Da Ni Za A Ďìnga Yada Sùññah, Kuma Na Yi Mafarki Na Ga Sheik Idris Dutsen Tanshi A Aljànnah, Inji Umar Ambato

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *