Monday, December 16
Shadow

‘Tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa’

Ministan Kuɗi na Najeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa tattalin arzƙin ƙasar na farfaɗowa, wanda hakan zai sa nan da ƴan watanni a daina samun hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar jama’a.

Mista Edun ya faɗi hakan ne a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels ta yi da shi, jiya Lahadi.

A rahotonta na watan Afirilu, kan farashin kayayyaki, Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar (National Bureau of Statistics) ta nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 33.20 cikin ɗari a watan Maris na wannan shekara — tashin ya ƙaru daga kashi 31.70 cikin ɗari a watan Fabarairu.

Hukumar ta ce tashin farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 40.01 cikin ɗari a cikin watan na Afirilu.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma'aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Duk da waɗannan alƙaluma da hukumar ta fitar, Ministan ya ce tattalin arzƙin Najeriyar na kan turba, yana mai ƙarin bayani da cewa kwalliya na biyan kuɗin sabulu sannu a hankali a kan sauye-sauye da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *