Tawagar Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ta yi hadari a garin Ihugh dake karamar hukumar Vandeikya dake jihar
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Lamari ya farune ranar Lahadi inda shaidun gani da ido suka ce daya daga cikin motocin tawagar gwamnan ce ta buge wani mutum ya mutu.
Lamarin ya farune yayin da gwamnan ya je gida yin hutun bikin kirsimeti.
Lamarin ya faru sau biyu ne a yayin da gwamnan ke zuwa gida da lokacin da yake dawowa.
Saidai me magana da yawun gwamnan, Solomon Iorpev ya musanta faruwar hadarin da tawagar gwaman, yace mota daya ce wadda aka bari a baya sauran motocin tawagar gwamnan sun wuce ta yi hadarin.
An tuntubi kakakin ‘yansandan jihar, SP Catherine Anene, saidai bata ce komai akan lamarin ba.