Friday, April 18
Shadow

Yanzu Adadin ‘Ya’yana Da Suka Sauke Kur’ani Sun Kai Biyar, Inji Jarumin Finfinan Hausa, Iliyasu Tantiri

Ga abinda Tantari ya bayyana bayan wasu yaransa biyu sun sauke Kur’ani “Alhamdulillah!!! Allah cikin Rahamarsa da amincewarsa, a yau Lahadi 29/12/2024 aka yi bikin saukar Karatun AL’QUR’ANI na ya’yana guda biyu, ABDULMUMIN ILYASU ABDULMUMIN DA RAHAMA ILYASU ABDULMUMIN.

“Yanzu Yarana biyar kenan suka sauke QUR’ANI da Izinin Ubangiji cikin su takwas da Allah Ya ba ni, ina alfahari da murna da wadannan yara matuka.

Ina godiya ga Allah S.W.T da ya ba ni ikon kulawa da su har suka kai wannan matsayi. Allah Ya sa su amfani musulunci da musulmai a duniya”.

Karanta Wannan  Yabon Tinubu ya kamata a yi game da cire tallafin man fetur ba zagi ba saboda sauran shuwagabanni Najeriyakasa cirewa suka yi amma shi ya cire>>Inji Hadiminsa, Sunday Dare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *