Wednesday, January 15
Shadow

Tinubu bai faɗi nawa albashi mafi ƙanƙanta zai kasance ba a jawabinsa

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta aike da ƙudiri ga Majalisar Dokokin ƙasar wanda zai kunshi adadin abin da aka amince da shi ya zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata a “matsayin wani ɓangare na “dokokinmu” a shekaru biyar ko ƙasa da haka masu zuwa.

Shugaban wanda ya faɗi hakan ne a yayin jawabinsa ga ƴan Najeriya albarkacin ranar dimukraɗiyya, ya ce lallai yana sane da halin matsin tattalin arzikin da ‘yan najeriyar ke ciki. To sai dai ya nemi “yan ƙasar da su tallafa wajen cimma “dimukraɗiyyar da za ta tabbatar da cigaban tattalin arziki.”

Ƴan Najeriya dai sun yi fatan jin ƙarin albashin da suka samu daga bakin shugaban nasu a jawabin nasa na safiyar Talata.

Karanta Wannan  Kalli Yanda sojojin kasar Yahudawan Isàèlà ke taka tutar kasar Saudiyya

A ranar Litinin ne dai kwamitin mutum 37 da aka kafa kan albashin mafi ƙanƙanta ya miƙa rahotonsa bayan kwashe kimanin watanni biyar da kafa shi.

Wakilan gwamnatin tarayya da na masana’antu masu zaman kansu dai da ke kwamitin na shugaban ƙasa domin tattauna batun albashin sun amince da naira 62,000, inda su kuma wakilan ƙungiyoyin ƙwadago suka kafe a naira 250,000.

Batun tsadar rayuwa da na ƙarancin albashi ya sa ma’aikata a Najeriya rashin nuna sha’awarsu ga bikin ranar dimukraɗiyya na bana da ake yi a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *