
Tinubu ya bar Japan zuwa ƙasar Brazil zai kuma yada zango a Los Angeles – Fadar shugaban ƙasa
Fadar shugaban ƙasa ta ce shugaba Bola Tinubu ya zarce Brazil bayan halartar taruka a Japan.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu zai hada zango a birnin Los Angeles na kasar Amurka kafin ya wuce birnin Brasilia na kasar Brazil domin ziyarar aiki da zai fara daga ranar 24 ga watan Agusta.