
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu zuwa jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a ziyarar – wadda zai fara ranar Juma’a – shugaban zai gana da masu ruwa da tsaki domin nazartar yanayin tsaro a jihar.
Sanarwar ta ce shugaban zai ƙaddamar da cibiyar ayyukan noma ta zamani da wani titi mai hannu biyu, mai tsawo kilomita 24 da gwamnan jihar, Dikko Radda ya kammala.
Haka kuma Bayo Onanuga ya ce Shugaba Tinubu zai kuma halarci ɗaurin auren ƴargidan gwamnan Katsinan kafin kammala ziyarar tasa a jihar.