Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba shi da wani zaɓi “da ya wuce” korar dubun dubatar baƙin haure da ba su da izinin zama a ƙasar.
Cikin wata tattaunawa da NBC ranar Alhamis, shugaban ya ce: “Ba magaanr abin da za mu samu ko rasawa ba ce. Ba haka ba ne – ba mu da wani zaɓi ne. Idan ana kashe mutane, jagororin ‘yanƙwaya na lalata ƙasashe, to yanzu za su koma ƙasashensu saboda ba za su zauna mana a nan ba.”
Ko da gwamnatin ta yi nasarar koro baƙin a hukumance, to za ta sha fama wajen yadda za ta aiwatar da hakan. Ƙwararru na ganin hakan zai laƙume biliyoyin dala kafin a iya mayar da mutum miliyan ɗaya gida.
A shekarar 2021 aka dakatar da shirin kai samame kan wuraren ayyukan baƙin, wanda gwamnatin Trump ta aiwatar.
Adadin mutanen da ake kamawa a cikin Amurka tare da mayar da su ƙasashensu bai wuce 100,000 ba cikin shekara 10, amma sun kai har 230,000 a shekara a farkon mulkin Barrack Obama.