
Tsadar rayuwa tasa masu motocin Alfarma masu tsada ciki hadda sojoji da ma’aikatan banki da sauransu sun koma yin haya da motocin nasu dan samun sauki.
Tun da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta cire tallafin man fetur, tsadar rayuwa ta kara kazancewa a Najeriya.
An zanta da wasu daga cikin ma’aikatan Gwamnati da suka koma daukar fasinja dan samun saukin rayuwa.
Jaridar Punchng tace wakiliyarta a Legas ta zanta da wasu daga cikin masu irin wannan sana’ar.
Akwai soja akwai ma’aikatan banki akwai ma ‘yan kasuwa da Sauransu wadanda jaridar ta zanta dasu inda suka bayyana cewa sukan dauki fasinjoji ne dan samun saukin musaman kudin Ma fetur, wasu kuma sun ce suna hakanne dan samun karin kudin da zasu kula da iyalinsu saboda albashi baya isarsu.
A baya da mun ga yanda Road Safety suka yi amfani da motarsu wajan daukar Fasinja a Abuja.