Wednesday, January 15
Shadow

TSADAR RAYUWA: Ga Abinda Ya Kamata Mu Yi Domin Samun Mafita

Daga Zainab Muhammad Yar Mitsila

…Ina roƙon don Allah a taimaka wa al’ummar mu a yaɗa (sharing) wannan saƙon

Wallahi ƙasa rnan fa sai talakawa sun tashi tsaye. Ni dai ba zan daina bada wannan shawari ba, mu faɗawa Limamanmu kowacce sallar asuba da ta Juma’a a tsaya da alqunut ya zamo kullum sai an yi.

Sannan ina baiwa magidanta da matan aure shawarin duk bayan sallar asuba mu zauna da yaranmu koda na minti 15 ne zuwa 20 mu yi istigfari sau 100 sai mu ɗaga hannu mu yi addu’a yaranmu suna amsawa da amin yã hayyu yã qayyum, Insha’allah Allah zai dube mu.

Karanta Wannan  Ba za mu taɓa yin sulhu da 'yan bindiga ba - Gwamnan Zamfara

Wannan abun Wallahi idan mun saka kanmu sam ba wani abune mai wahala ba.

Allah Ya kawo mana ƙarshen duk wani źàĺùñçi, kuma mu guji karɓar kuɗi ko taliya da zani lokacin zaɓe, mu zaɓi mutane nagari koda ba su da ko sisi, mu dogara da Allah ya isar mana.

Wallahu a’alam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *