Saturday, December 28
Shadow

Tsageran ESN Sun kashe sojojin Najeria biyu daya ya bace, sun kuma tsere da makaman sojojin

Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin ta 2 bayan harin da kungiyar ESN dake karkashin kungiyar IPOB ta kai mata.

A sanarwar data fitar ranar Asabar, Hukumar sojojin ta bayyana cewa, lamarin ya farune a garin Osina dake karamar hukumar Ideator ta Arewa dake jihar Imo a yayin da wata tawagar sojojin ke dawowa daga wani dauki da suka kai a yankin Osina bayan kiran da aka musu cewa kungiyar ta ESN ta kai hari garin.

Hakanan sanarwar tace sojojin sun fafata da ESN a yankin Nkwachi inda suka kashe mutum daya daga ciki sauran suka tsere sannan kuma an kwato bindiga daya aga hannunsu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo inda wani mutum ke cewa yayi lalata da mata 315 a wannan shekarar ta 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *