Friday, December 5
Shadow

Tshàgyèràn Dhàjì da suka dàukì daliban jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami’an saro, ba’a biya kudin Fànsà ba>>Inji Majalisar Dattijai

Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, ‘yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami’an tsaro.

Me magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai.

Yace ba’a biya kudin fansa ba kamar yanda ake yamadidi.

Yace kuma wai dan ba’a ga an kama kowa ba ko ba’a ga gawar wadanda suka yi garkuwa dasu din ba, hakan ba yana nufin ba’a yi fadan ba.

Yace sannan kuma Ba dole bane sai jami’an tsaro sun sanar da yanda suka kubutar da daliban ba, kawai dai ana son a kubutar dasu kuma an kubutar dasu din.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Wani mutum da ya taba taimakon wannan matar da Naira dubu dari biyar da hamsin yayi mamakin ganinta tana bara da 'ya'yanta akan titi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *