Tuesday, January 7
Shadow

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi karin haske kan maganar komawarsa PDP

A dazu ne rade-radi suka watsu sosai a kafafen sada zumunta cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yanki katin shiga Jam’iyyar PDP a Unguwar Sarki Kaduna.

A wancan lokacin ba’aji wata sanarwa daga bakinsa ba ko Jam’iyyar ta PDP.

Mutane da yawa sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta akan labarin inda wasu ke ganin hakan ba abin mamaki bane ganin yanda Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta APC ta mayar da El-Rufai saniyar ware.

Idan dai za’a iya tunawa, Gwamna El-Rufai na daya daga cikin na gaba-gaba da suka dage sai Tunubu ya zama shugaban kasa kuma bayan an kafa Gwamnatin Tinubu, ya bayar da sunanshi cikin wadanda zai baiwa Ministoci amma Sai El-Rufai ya kasa tsallake tantancewar majalisa.

Karanta Wannan  Babu Wani Sulhu Da Za Mu Yi Da 'Ýan Biñdiga, Inji Gwamnatin Zamfara

Tun bayan nan ne dai aka fara takun saka tsakanin El-Rufai da Gwamnatin Tinubu.

Hakanan a jiharsa ta Kaduna ma inda yayi ruwa yayi tsaki dan ganin Uba Sani ya zama Gwamna, shima akwai kullalla tsakaninsa da Gwamna Uba sani inda ake zargin Gwamnatin El-Rufain da batar da kudaden talakawa.

Na bayabayannan shine kama tsohon shugaban ma’aikatansa kuma Kwamishinan kudi a zamanin mulkinsa, Bashir Saidu bisa zargin almubazzarancin sama da Naira Biliyan 4.

Dalilin hakane ma yasa koda mutane suka ji cewa El-Rufai ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa PDP basu yi mamaki ba.

El-Rufai a martaninsa ta kafar X wadda a baya aka fi sani da Twitter, ya bayyana cewa ba gaskiya bane maganar komawarsa PDP, inda yace ya baiwa lauyoyinsa umarnin daukar mataki akan lamarin.

Karanta Wannan  Gane Mini Hanya: Babu yarjejeniyar karɓa-karɓa a tsakanina da Atiku - Kwankwaso

Hakanan wani Hadiminsa da aka yi hira dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV ma ya musanta lamarin inda yace El-Rufai ba zai koma PDP ba tare da sanarwar hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *