Monday, March 16
Shadow

Tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige ya nemi Beli inda yace yana fama da rashin lafiya bayan da kotu tace a tsareshi a gidan yarin Kuje, amma EFCC tace kada a bada belinsa dan zai iya tserewa

Tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige ya nemi Beli bayan da Kotu tasa a daureshi a gidan yarin Kuje.

Yace yana fama da rashin lafiya, kamar yanda Lauyansa, Patrick Ikwueto ya bayyanawa me shari’a ta babbar kotun tarayya dake Gwarimpa a Abuja Justice Maryam Aliyu Hassan

Saidai Lauyan EFCC, Sylvanus Tahir, SAN yace kotun kada ta bayar da belinsa dan a baya ita EFCC ta sakeshi inda aka saka mai ranar da zai sake komawa dan ci gaba da bincike amma yaki komawa.

Yace tsohon Ministan ka iya tserewa idan aka bayar da belinsa.

Saidai Mai shari’a Maryam Aliyu Hassan tace a ci gaba da tsare Ngige a gidan yarin kuje har ranar 18 ga watan Disamba kamin ta yanke hukunci kan maganar Belin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Tsohon da aka ruwaitoshi yana cewa shine ya gina kabarin Shugaba Buhari, a yanzu ya fito ya ce karya yake bashine ya gina kabarin ba, saidai an zargi cewa tursasashi aka yi ya fadi hakan bayan da yace ba'a biyashi kudin ginin kabarin da yayi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *