Thursday, February 5
Shadow

Tsohon soja ya mùtù a hannun ‘Yàn Bìndìgà duk da biyan Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fansa

Rahotanni daga jihar Kogi na cewa, wani tsohon soja me suna Major Joe Ajayi ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane duk da danginsa sun biya kudin fansarsa Naira Miliyan 10.

An yi garkuwa dashine a gidansa dake Odo-Ape na karamar hukumar Kabba-Bunu ranar May 21, 2025 da misalin karfe 11:30pm.

Da farko dai wanda suka yi garkuwa dashi sun nemi Naira Miliyan 50 inda daga baya da suka ga bashi da lafiya zai rasu.

Sai suka ce a kai musu Naira Miliyan 10, bayan da aka kai musu, suka bayyana inda za’a je a daukeshi, sai gawarsa aka tarar.

Tuni aka kai gawar tasa zuwa mutuware dake Asibitin Kabba Specialist Hospital.

Karanta Wannan  Kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya ta lashe kofin Kwallon Kwando na mata na Afrika

Masu garkuwa da mutane sun matsawa jihar Kogi a ‘yan kwanakinnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *